Skip to main content

Posts

Showing posts from December, 2022
  Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibi Aminu Muhammad Daga WAKILINMU Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin nan Mohammed Aminu bayan da ta sha caccaka da tofin Allah wadai daga ɓangarori daban-daban. Lauyan Aisha, Fidelis Ogbobe ya ce Aisha ta janye ƙarar ne bayan da wasu manyan ƙasa suka sa baki cikin batun. Ya ce ta janye ƙarar ne ta hanyar kafa hujja da Sashe na 108 da ƙaramin sashe na 2(a) na Dokar Manyar Laifuka. Da yake yanke hukuncin kan batun, Alƙalin Babbar Kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya yaba wa Aisha Buhari dangane da haƙuri da afuwar da ta yi tare da janye ƙarar zargin da ɗalibi Aminu ya yi mata. Daga nan, Alƙalin ya yi jan hankali kan iyaye su riƙa kulawa da ‘ya’yansu yadda ya kamata gudun sake aukuwar makamancin abin da Aminu ya aikata. Aisha ta maka ɗalibin a kotu ne kan zargin ɓata mata suna. Aminu wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ya ci na jaki a hannun jami’an tsaro bay...
Ba za mu kara kudin man fetur ba a yanzu - Gwamnatin Tarayya Daga WAKILINMU  Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar ƙara kuɗin man fetur "a wannan lokaci" yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fama da dogayen layi a gidajen man. Wata sanarwa da hukumar kula da rarraba fetur ta NMDPA ta fitar ta ce ya zama dole su musanta jita-jitar da ake yi game da farashin man da kuma ƙarancinsa a cikin Najeriya. Sanarwar ta ce kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya tanadi man fetur da zai isa amfanin ƙasar tsawon kwana 34. "Ana bai wa 'yan kasuwa da sauran jama'a shawarar su daina fargaba da kuma sayen man don karkatarwa da kuma ɓoye shi," in ji NMDPR. Bisa al'ada, akan fuskanci ƙarancin man fetur a duk ƙarshen shekara a Najeriya duk da cewa a baya-bayan nan ba a ga hakan ba sakamakon ƙarin kuɗin man da gwamnati ta dinga yi akai-akai. Sai dai wannan karon an fara ƙarancin fetur ɗin tun daga tsakiyar 2022, inda wasu gidajen mai ke sayar da lita ɗaya kan N200 zuwa...

Gwamnatin Najeriya Ta Gargadi 'Yan Siyasa Wajen Amfani Da 'Yan Daba

Gwamnatin Najeriya Ta Gargadi 'Yan Siyasa Wajen Amfani Da 'Yan Daba Daga Abbakar Aleeyu Anache  Gwamnatin Najeriya ta gargadi Gwamnonin jihohin kasar 26 da su kaucewa yin amfani da yan bangar siyasa wajen hana abokan hamayyarsu gudanar da tarurrukan yankin neman zabe musamman ganin lokacin zaben shekara mai zuwa na karatowa,  Mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya gabatar da wannan gargadi inda yake cewa an baza jami'an tsaro a fadin kasar domin murkushe duk wani yunkurin haifar da tashin hankali wajen zaben mai zuwa,  Monguno yace abin takaici ne yadda Gwamnonin ke amfani da karfin mulki wajen tirsasawa abokan adawarsu maimakon gabatar da ayyukan da suka yi domin janyo hankalin masu kada kuri'u su zabi wadanda suke marawa baya, Rahotanni sun ce jam'iyyun adawa na cigaba da fuskantar matsaloli sosai wajen tallata yan takararsu ta hanyar manna fastoci ko ta kafofin yada labarai ko kuma gudanar da tarurruka...