FYADE Mene Ne Fyade ? Amsa : To a takaicen takaitawa fyade dai shi ne yin amfani da mace ba tare da izini, yarda, ko son ranta ba; ta hanyar amfani da karfi, ko dubarbaru ko kawar da tunani ko kuma wani abu makamancin hakan. Mene Ne Ke Jawo Yawaitar Fyade? Amsa: Daya daga cikin abubuwan da suke jawo yawaitar fyade sun hada da: Sa kayan banza da wasu mata ke yi, wanda ire-iren wadannan kayan da matan ke sawa a cikin gari suna ratsa unguwanni yana taimakawa kwarai da gaske wajen jawo hankalin wadansu mazajen musamman ashararai, masu shaye-shaye, da kuma wadanda ba sa zama don jiran komai sai don irin wannan damar, wato 'yan iska, wadanda dama aikinsu ke nan; Mai son zuwa fada ne dama, to bare kuma sarki ya yi kira, ai kawai sai tafiya. Don haka ire-iren wadancan mutanen da na zaiyano a baya suna samun wata 'yar dama ko yaya take, sai su yi amfani da ita waje...