Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibi Aminu Muhammad Daga WAKILINMU Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin nan Mohammed Aminu bayan da ta sha caccaka da tofin Allah wadai daga ɓangarori daban-daban. Lauyan Aisha, Fidelis Ogbobe ya ce Aisha ta janye ƙarar ne bayan da wasu manyan ƙasa suka sa baki cikin batun. Ya ce ta janye ƙarar ne ta hanyar kafa hujja da Sashe na 108 da ƙaramin sashe na 2(a) na Dokar Manyar Laifuka. Da yake yanke hukuncin kan batun, Alƙalin Babbar Kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya yaba wa Aisha Buhari dangane da haƙuri da afuwar da ta yi tare da janye ƙarar zargin da ɗalibi Aminu ya yi mata. Daga nan, Alƙalin ya yi jan hankali kan iyaye su riƙa kulawa da ‘ya’yansu yadda ya kamata gudun sake aukuwar makamancin abin da Aminu ya aikata. Aisha ta maka ɗalibin a kotu ne kan zargin ɓata mata suna. Aminu wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ya ci na jaki a hannun jami’an tsaro bay...
Ba za mu kara kudin man fetur ba a yanzu - Gwamnatin Tarayya Daga WAKILINMU Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar ƙara kuɗin man fetur "a wannan lokaci" yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fama da dogayen layi a gidajen man. Wata sanarwa da hukumar kula da rarraba fetur ta NMDPA ta fitar ta ce ya zama dole su musanta jita-jitar da ake yi game da farashin man da kuma ƙarancinsa a cikin Najeriya. Sanarwar ta ce kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya tanadi man fetur da zai isa amfanin ƙasar tsawon kwana 34. "Ana bai wa 'yan kasuwa da sauran jama'a shawarar su daina fargaba da kuma sayen man don karkatarwa da kuma ɓoye shi," in ji NMDPR. Bisa al'ada, akan fuskanci ƙarancin man fetur a duk ƙarshen shekara a Najeriya duk da cewa a baya-bayan nan ba a ga hakan ba sakamakon ƙarin kuɗin man da gwamnati ta dinga yi akai-akai. Sai dai wannan karon an fara ƙarancin fetur ɗin tun daga tsakiyar 2022, inda wasu gidajen mai ke sayar da lita ɗaya kan N200 zuwa...